Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta yi wa mukaddashin kwamandan Soji kwanton-bauna

Mayakan Boko Haram sun kai hari a kan ayarin motar wani mukaddashin kwamandan soji Victor Ezugwu dake kan hanyarsa ta kai ziyara a sansanin soji a garin Bama na jahar Borno.

Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES
Talla

Kakakin Rundunar sojin kasa, Kanal Sani Usman Kukasheka, ya tabbatar da mutuwar Soji guda da kuma wasu soji 2 da suka samu raunika, sai dai ya ce sojojin sun ci karfin mayakan inda suka yi nasarar kashe wasu daga cikinsu tare da karbe wasu makamai da motar kirar Hilux.

Wannan harin dai bai hana Janar Ezugwu kai ziyarar garin na Bama ba, yayin da aka mayar da gawar sojin daya mutu da sauran wadanda suka ji rauni garin Maiduguri.

Kanar kukasheka ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba, har sai sun ga karshen kungiyar Boko Haram.

Harin na yau talata na zuwa ne kwana guda bayan aukuwar wata munmunar arangama tsakanin rundunar soji da mayakan Boko Haram a jahar Borno.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.