Isa ga babban shafi
Boko Haram

Yawan amfani da yara ya karu a hare haren Boko Haram

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce adadin yara kanana da kungiyar Boko Haram ke amfani da su domin kai hare-haren ta’addanci ya rubayya da kusan sau 10 daga 2014 zuwa 2015 musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Sojojin Najeriya sun kori 'Yan Boko Haram a Sambisa tare da kawato makamai
Sojojin Najeriya sun kori 'Yan Boko Haram a Sambisa tare da kawato makamai via SK Usman facebook
Talla

Doune Porter mai magana da yawun asusun na Unicef, tace Adadin yara da kungiyar ke amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake ya rubayya kusan har sau 10 a cikin shekarar da ta gabata, hakan na faruwa ne a jihohin arewa maso gabashin Najeriya inda wannan kungiyar ta fi gudanar da ayyukanta, da kuma kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da ke fama da Boko Haram.

Tace sun fahimci cewa adadin ya tashi daga yaro 4 a shekara ta 2014 zuwa yaro 40 a cikin shekarar da ta wuce, wannan kuam a cewarta lamari ne da ke matukar tayar da hankali.

Sannan tace sama da kashi 75 cikin Yaran da ke kai hare haren Mata ne.

Porter tace ka da a yi zaton cewa yaran da ake amfani da su wajen kai harin suna shawar yin haka ne, sam ba haka ba ne domin kuwa ana cutar da su ne, kananan yara ba za su iya fahintar illar hakan ba, abin da ke tabbatar da cewa ana amfani da su ne da karfi domin kai hare-hare da bam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.