Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Boko Haram sun yadu cikin jama’a

Rundunar sojin Najeriya ta ce sakamakon tsanantar hare-hare ta sama da kasa akan maboyar ‘yan Boko Haram da ke cikin gandun dajin Sambisa, yanzu haka mayakan kungiyar na ci gaba da tserewa domin barin yankin.

An tsaurara matakan tsaro a sansanonin 'Yan gudun hijira a Kamaru
An tsaurara matakan tsaro a sansanonin 'Yan gudun hijira a Kamaru REUTERS
Talla

Sanarwar da rundunar sojin Najeriyar ta fitar ta bukaci jama’a da su yi takantsantsan tare da gaggauta sanar da hukumomin tsaro matukar suka ga wani mutum da suke zargin dan Boko Haram.

Sanarwar tace akwai alamun da ke tabbatar da wasu daga cikin ‘yan kungiyar ta Boko Haram na kokarin tserewa daga Sambisa ne domin sajewa a cikin jama’a.

Rundunar Sojin ta Najeriya ta fadi a cikin sanarwar cewa zata kare hakkin dukkan bayanan sirrin da ta samu na Jama’a akan ‘Yan Boko Haram tare da shan alwashin murkushe wadanda suka rage.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.