Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun ECOWAS zata saurari Koken Dasuki

Kotun kungiyar kasashen yankin Yammacin Afirka ECOWAS ta amince ta saurari karar da tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Sambo Dasuki ya shigar a gabanta, yana mai zargin kamawa da tsare shi da aka yi a matsayin abin da ya sabawa ka’ida.

Kanal Sambo Dasuki tsohon mai ba Shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro
Kanal Sambo Dasuki tsohon mai ba Shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro AFP
Talla

Mai shara’a Friday Chijoke Nwoke daya daga cikin alkalai 7 na kotun, ya ce za su duba wannan batu na zargin tauye hakki da Dasuki ya gabatar ma ta.

Kanal Sambo Dasuki na tsare ne tun a watan Disemba saboda zargin handame Biliyoyan kudade da aka ware domin sayo wa sojan Najeriya makaman yaki da mayakan Boko Haram da suka kashe dubban mutane a arewa maso gabashin kasar.

Alkalin kotun ta ECOWAS ya ce wanda ya shigar da kara na neman samun ‘yancinsa ne na walwala.

Kotun kuma tace zata saurari bangaren Gwamnatin Najeriya ko suna da ja game da bukatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.