Isa ga babban shafi
Najeriya

An gano rumbun abincin mayakan Boko Haram a Borno

Rundunar sojin kasa dake kokarin ganin bayan kungiyar Boko Haram sun yi kicibus da rumbun abincin mayakan a yankin karamar hukumar Bama dake a jahar Borno a lokacin da suka kai samame wasu kauyuka da niyyar fatatakar sauran mayakan da suka yi saura a yankin

Soldats nigérians dans le village de Baga (Etat de Borno).
Soldats nigérians dans le village de Baga (Etat de Borno). REUTERS/Tim Cocks
Talla

Rundunar Sojin ta kuma gano yadda mayakan ke labewa a saman bishiyoyi inda suke iya hango dakarun sojin kasar daga nesa inji kakakin rundunar kasar kanar Usman Kukasheka da yake jawabi bayan gano mabuyar kungiyar

kanar Ousman ya kara da cewa ainihi ma dai dakarun sun kai samame wasu kauyukan dake karamar hukumar Bama a jahar Borno da niyyar kakkabe sauran mayakan dake boye a wasu garuruwan yankin kafin su kai ga wannan nasarar gano rumbun abincin da mayakan suka yi a karkashin kasa

Dakarun sojin sun yi nasarar kashe mayakan kungiyar 2 tare da kwato bindigogi kirar Ak47 guda 3, sun kuma yanto wasu yara 2 a hannun mayakan kungiyar ta Boko Haram
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.