Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta hanawa Yara Miliyan guda karatu

Hukumar UNICEF da ke kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya tace rikicin Boko Haram ya haramtawa yara sama da miliyan gudazuwa makaranta domin samun ilimi, tare da bayyana damuwar akan makomar yaran a nan gaba.

Wasu dalibai a wata Makaranta da Mayakan Boko Haram suka kona a garin Maiduguri
Wasu dalibai a wata Makaranta da Mayakan Boko Haram suka kona a garin Maiduguri AFP
Talla

Rahotan hukumar ya nuna cewar makarantu sama da 2,000 yanzu haka suke rufe a kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma Nijar, sannan daruruwa ne aka lalata a hare haren da Boko Haram ta kai.

A makon gobe ne ake saran wa’adin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin kasar na murkushe kungiyar zai cika, sai dai UNICEF tace koda an samu nasarar yin haka gwamnatocin Najeriya za su fuskanci matsaloli dangane da wadannan dimbin yaran da ba su zuwa makaranta.

Daraktan UNICEF a Yankin Afrika ta Yamma da Afirka ta Tsakiya Manuel Fontain ya ce ci gaba da zaman yaran ba tare da zuwa makaranta ba wata dama ce da kungiyoyi za su dauke su don yin amfani da su ta hanyar da ba ta kamata ba.

Tun kaddamar da yaki a 2009, kungiyar Boko Haram ta kai hare hare da dama a Makarantu tare da sace dalibai musamman daliban Makarantar Mata a Chibok 276 da kungiyar ta yi awon gaba su, wanda ya ja hankalin duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.