Isa ga babban shafi
Boko Haram

Sojoji sun kashe ‘Yan Boko Haram 12

Sojojin Najeriya sun kashe ‘Yan Boko Haram 12 tare da kwato makamai da dama daga hannun Mayakan a yankin Damboa cikin Jihar Borno arewa maso gabashin kasar.

Kanal Usman Kukasheka Kakakin Sojin Najeriya
Kanal Usman Kukasheka Kakakin Sojin Najeriya via twitter
Talla

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Sojin Najeriya Kanal Sani Usman Kukasheka ya ce jami’an Sojinsu sun kashe mayakan ne a lokacin da suke gudanar da aiki tsakanin sabon gari zuwa Damboa.

Kuma cikin mayakan da aka kashe har da shugabansu Ameer a Bulagaya. Sannan a ranar lahadi sojojin sun kashe ‘yan boko haram 9 a kauyen Mainari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.