Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta bada belin Dasuki

Babbar kotu a Abuja ta bayar da belin toshon mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro Sambo da Dasuki tare da da wasu mutane guda hudu da ake zargi da satar kudaden sayo makamai domin yaki da Boko Haram a Najeriya.

Kanal Sambo Dasuki tsohon mai ba Shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro
Kanal Sambo Dasuki tsohon mai ba Shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro AFP
Talla

Mai shari’a Hussiani Baba Yusuf ne ya bada belin Dasuki akan kudi Naira Miliyan 250.

Sannan ya bukaci kwafi na fasfo din shi tare da sanar da kotun duk lokacin da zai bar Abuja.

Ana zargin Sambo Dasuki da yin fatali da kudade sama da dala Biliyan biyu da aka ware domin sayo makaman yaki da Boko Haram da suka kashe dubban mutane a arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.