Isa ga babban shafi
Boko Haram

Boko Haram na shirin sace dalibai a makarantu

Hukumomin Najeriya sun yi gargadin cewa Mayakan Boko Haram na shirin sace daliban makaranta kafin cikar wa’adin da shugaba Muhammadu Buhari ya dibar wa Sojin kasar na murkushe mayakan.

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed via royaltimes
Talla

A cikin wata sanarwa, Ministan yada labarai da al'adu, Lai Muhammad ya bukaci makarantu su inganta tsaro domin akwai yiyuwar ‘Yan Boko Haram za su abkawa makaratun domin sace dalibai kamar yadda ta faru a Chibok inda suka sace dalibai 276 a 2014.

Sannan sanarwar ta gargadi ‘Yan kasashen waje su yi taka tsantsan domin ‘Yan Boko Haram sun talauce yanzu suna neman hanyoyin arzuta kanssuu ta hanyar kudaden fansa.

Shugaban Najeriya ya sha alwashin murkushe Boko Haram kafin karshen shekarar 2015.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.