Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane 14 a Borno

Kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane 14 a wani harin da ta kaddamar a kauyen Kamuya na jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda ta fille kawunan wasu daga cikinsu yayin da ta harbe sauran da bindiga.

Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai hari a Najeriya duk da kokarin hukumomin kasar na kawo karshen kungiyar.
Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai hari a Najeriya duk da kokarin hukumomin kasar na kawo karshen kungiyar. AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Mazauna kauyen sun bayyana cewa al-amarin ya faru ne da misalin karfe 8 agogon kasar na daren jiya, kuma mayakan kungiyar sun yi amfani da kekuna ne wajan shiga kauyen.

Ibrahim Babangana, mazaunin Kamuya ne ya kuma shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa, jama’ar kauyen sun gudu Biu domin tsira da rayukansu yayin da mayakan suka cinna wa kauyen nasu wuta.

Tuni dai aka yi jana’izar mutanen da suka hallaka a kazamin harin amma wadanda suka jikkata na kwance a asibiti domin kula da lafiyarsu.

Kamuya dai, nan ne kauyan mahaifiyar shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.