Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Gwamnatin Borno na ci gaba da gine-gine

Gwamnatin jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, na ci gaba da gina wuraren da kungiyar Bokmo Haram ta kona a fadin jihar.

Gwamnan Jihar Borno Kashim shettima a lokacin da ya ke kai ziyara a Baga da ke jihar.
Gwamnan Jihar Borno Kashim shettima a lokacin da ya ke kai ziyara a Baga da ke jihar. REUTERS
Talla

Gwamnan jihar ne Kashim Shettima ya tabbatar wa manema labarai haka a lokacin da ya gana da su a yammacin jiya bayan kammala ran gadin makarantu da masallatai da kasuwanni da asibitocin da ake sake ginawa.

Shettima ya ce, suna sa ran kammala wani sashi na wadannan ayyukan nan da karshen wata mai zuwa.

Gwamann ya ce Allah kadai ya san abinda suka kashe na kudade wajen gudanar da ayyukan amma a garin Kaga kadai sun kashe sama da miliyan 500.

Rikicin Boko Haram ya tilasta wa dubun dubatan jama’a kaurace wa gidajensu a jihar Borno.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.