Tafkin Chadi
An kashe mutane 27 a hare haren kunar bakin wake a tafkin Chadi
Akalla mutane 27 Sun mutu yayin da wasu 80 suka jikkata a wasu jerin hare haren kunar bakin wake guda uku da aka kai a yankin tafkin Chadi a ranar Assabar. Ana daura alhakin hare-haren akan mayakan Boko Haram.
Wallafawa ranar:
Talla
Wata majiyar Sojin Chadi ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa ‘yan kunar bakin waken sun kai hare-haren ne a wurare daban daban cikin wata kasuwar Loulou Fou da ake ci mako mako.
Mayakan Boko Haram dai sun dade suna addabar Yankin tafkin Chadi wanda ke cikin dokar ta-baci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu