Isa ga babban shafi
Kamaru

Boko Haram ta kashe mutane 3 a Fotokol, cikin Kamaru

Wasu mata biyu sun tayar da bam a wani Masallaci da ke Kamaru inda suka hallaka mutane 3 a garin Fotokol yankin arewa mai nisa a kasar Kamaru. Rahotanni sun ce daya daga cikin ‘yan matan ta yi nasarar tayar da bam din kusa da Masallacin yayin da aka harbe abokiyar tafiyarta.

Yankin Fotokol a arewacin Kamaru mai fama da hare haren Boko Haram
Yankin Fotokol a arewacin Kamaru mai fama da hare haren Boko Haram AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Irin wannan harin ne ‘Yan matan suka kai a Chadi inda mutane hudu suka mutu tare da raunana 14 a garin Ngouboua a ranar Lahadi.

Harin Fotokol da aka kai a Fotokol a ranar Litinin, shi ne karo na 16 a yankin arewacin Kamaru tun a watan Yuli.

Duk da ana samun galaba akan Mayakan Boko Haram da ke da alaka da mayakan IS masu da’awar jihadi a Syria da Iraqi amma sun bullo da salon kai hare haren kunar bakin wake wadanda mata ke kai wa a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.