Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun 'yanto mutane 338 daga hannun Boko Haram

Rundunar tsaron tarayyar Najeriya ta sanar da ‘yanto mutane 338 daga hannun’yan kungiyar Boko Haram, sakamakon wani farmaki da jami’an tsaron suka kai a cikin gandun dajin Sambisa.

Sojoji da wasu fararen hula a dajin Sambisa
Sojoji da wasu fararen hula a dajin Sambisa AFP PHOTO / NIGERIAN ARMY
Talla

Sanarwar da rundunar tsaron ta fitar na cewa 138 daga cikin mutanen da aka ceto mata ne, yayin da 192 suka kasance kananan yara.

 

Hakazalika rundunar tsaron ta tabbatar da cewa jami'anta sun kashe 'yan Boko Haram sama da 30 a lokacin wannan farmaki.

Babban kwamandan rundunar sojan kasa a Najeriya Janar Tukur Buratai, ya kai ziyara a bataliyar sojan kasar ta 28 da ke garin Mubi a jihar Adamawa inda ya jagoranci bikin karamma sojojin kasar 2900 a matsayin karfafa masu gwiwa a kokarin da kasar ke yi na kawo karshen Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.