Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan Boko Haram sun kama garin Kerewa na arewacin Kamaru

A kasar Kamaru, mayakan Boko Haram sun kama garin Kerewa da ke kusa da iyakar kasar da Najeriya, bayan da suka yi nasarar fatattakar jami’an tsaron kasar.

Jami'an tsaron Kamaru da ke fada da 'yan Boko Haram
Jami'an tsaron Kamaru da ke fada da 'yan Boko Haram RFI/Nicolas Champeaux
Talla

Wannan ne dai karo na farko a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan da mayakan na Boko Haram suka yi nasarar kwace wani yanki a cikin Kamaru, kasar da ke taimaka wa Najeriya a yakin da take da magoya bayan wannan kungiya.

Kerewa dai gari ne mai kunshe da mutane sama da dubu 50, kuma wasu majiyoyi sun ce an samu asarar rayukan fararen hula da jami’an tsaron kasar da dama a lokacin da ‘yan bindigar ke kokarin kama garin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.