Isa ga babban shafi
FIFA-CAF

Shugaban Fifa Issa Hayatou ya kai ziyara a Kamaru

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya na wucin gadi Issa Hayatou ya isa kasar Kamaru a jiya asabar,ziyayar da yayi amfani da ita domin ganawa da manema labarai. An dai zabi Issa Hayatou ne bayan matakin da kwamitin da’a na hukumar FIFA ya dauka na dakatar da Sepp Blatter har na tsawon watanni uku a matsayin shugaban hukumar ta FIFA sakamakon zarginsa da hannu a badakalar cin hanci da rashawa a hukumar. 

ISSA Hayatou,Shugaban wucin gadin hukumar kwallon kaffar FIFA.
ISSA Hayatou,Shugaban wucin gadin hukumar kwallon kaffar FIFA. AFP PHOTO / FABRICE COFFRINI
Talla

Har ila yau kwamitin ya dakatar da Michel Platini, shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai saboda zargin da shi ma ake masa na karban kudade daga hannun Blatter ba bisa ka’ida ba.

Hayatou dai na fama da matsalar koda yayin da wata sanarwa da ta fito daga hukumar kwallon kafa ta Afrika ta ce, wannan matsalar ba ta hana shi jagorancin hukumar kwallon kafa ta Afrika ba, don haka, ba za ta hana shi gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa ba a matsayinsa na shuganban FIFA na wucen gadi.

Issa Hayatou mai shekaru 69, ya karbi ragamar FIFA ne a matsayinsa na babban mataimakin Sepp Blatter,wanda a jawabin sa ta kaffar talabijen din kasar Kamaru ya tabbatar da cewa ba shi da hannu ko masanniya a batun badakala dake wakana a Fifa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.