Isa ga babban shafi
Amurka

Boko Haram: Amurka za ta tura sojoji 300 Kamaru

Shugaban kasar Amurka Barack Obama zai aika sojoji 300 domin sa ido da kuma tattara bayanan sirri kan mayakan Boko Haram a kasar Kamaru.

Sojojin Amurka za su sa ido kan mayakan Boko Haram a Kamaru.
Sojojin Amurka za su sa ido kan mayakan Boko Haram a Kamaru. REUTERS/Romeo Ranoco
Talla

A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar, shugaba Obama ya ce, tuni aka tura sojoji 90, lamarin da ke nuna irin kaimin da Amurka ta kara wajan yaki da Boko Haram mai ikirarin alaka da kungiyar ISIS.

To sai dai sanarwar ta kara da cewa, sojojin na Amurka ba za su shiga fafatawar da ake yi da Boko Haram ba, amma za a ba su makamai domin kare kansu.

Sojojin za su ci gaba da aiki a Kamaru har zuwa lokacin da za a ce ba a bukatar taimakonsu kamar yadda Shugaba Obama ya sanar.

Kamaru dai na cikin kasashen yankin tafkin Chadi dake fama da hare haren Boko Haram wadda ta kashe dubban mutane.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.