Isa ga babban shafi
Amnesty-BH-Kamaru

Sojoji da Boko Haram sun yi barna a Kamaru

Kungiyar Kare hakkin Bil’adama ta Amnesty Internationale ta ce rikicin kungiyar Boko Haram ta hallaka akalla Fararan hula 400 a Arewacin kasar Kamaru, yayin da wasu da dama ke ci gaba da mutuwa a hannun Jami’an tsaron kasar. 

© Xavier de Torres
Talla

Rahoton da Kungiyar ta fitar yau a birnin Younden na kasar Kamaru na cewa Dakarun kasar Kamaru sun mai da martini wajen kai samame kauyukan da ke kan iyakan kasar da Najeriya, inda aka kama mutane sama da 1000 da suka hada da kanana yara da shekarun su bai haura 5 ba.

A cewar Amnesty mutane 25 da jami’an tsaron Kamaru ke tsare da su, sun mutu yayin da wasu Karin mutanen 130 babu duriyar su har yanzu.

Alioune Tine Daraktan Amnesty mai kula da yammaci da tsakiyar Africa ya ce Mayakan Boko Haram na ci gaba da fantsama daga Najeriya zuwa cikin Kamaru, wanda ke sanadi mutuwar fararen hula.

Kungiyar Amnesty dai na cewa yadda Boko Haram ke kashe mutane, da bar na ta kaddarorin jama’a, da sace mutane da amfani da kananan yara wajen kai harin kunar bakin wake na kara bayyana cewa Kungiyar Boko Haram babu shaka ta aikata laifukan yaki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.