Isa ga babban shafi
Kamaru

Watanni uku da kama wakilin rfi Hausa a Kamaru

Gwmanatin kasar Kamaru ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da Ahmad Abba wakilin sashen Hausa na rediyo Faransa rfi da ke garin Maroua a gaban Kotu, bayan da ya share tsawon watanni uku a tsare ba tare da an bai wa lauya ko iyalansa damar ganawa da shi ba.

Tambarin rfi
Tambarin rfi
Talla

Ministan sadarwa na kasar Issa Bakary Tchiroma, ya shaida wa gidan rediyon RFI cewa, ko shakka babu ana tsare ne da Ahmad Abba a garin Yaounde, bisa zargin yin alaka da kungiyar Boko Haram, to sai dai bai bayyana lokacin da za a gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Da farko dai lauyan wanda ake zargin mai suna Charles Tchounga, ya ce ya damu matuka sakamakon yadda hukumomi suka hana shi ganawa da wanda ake zargin yau watanni uku kenan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.