Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Goodluck ta ci amana- Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, tsohuwar gwamnatin kasar ta Goodluck Jonathan ta kashe biliyoyin Naira da miliyoyin Dala wajen samar da kayayyaki ga rundunar sojin kasar domin yaki da kungiyar Boko Haram, amma duk da haka akwai cin amana.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Buhari ya ce, cin amanar ya yi sanadiyar salwantar rayukan al-umma da kayayyakin soji.

Shugaban ya fadi haka ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a gaban mambobin majalisar wakilai ta kasar a jiya laraba.

Shugaban ya bukaci ‘yan majalisar da su hada kai da majalisar zantarwa ta gwamnatin tarayya domin ceto kasar da kuma kula da ita yadda ya kamata.

A cewar Buhari, babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta ta fannin tsaro shi ne barazanar da kungiyar Boko Haram ke yi wa kasar amma ya ce, gwamnatinsa ta fitar da wasu sabbin shirye shirye dangane da horar da sojojin kasar tare da ba su makamai domin kawo karshen Boko Haram.

Ana dai zargin wasu daga cikin manyan jami'an tsohuwar gwamnatin da yin sama da fadi da kudaden da aka ware domin siyan makaman yaki da Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.