Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram na sarrafa takin zamani don yin man fetur

Rundunar Sojin Najeriya shiya ta 7 dake yaki da Mayakan Boko Haram a garin Maiduguri a jihar Borno dake arewacin kasar, ta gargadi manoma da ‘yan kasuwa masu musayar sinadarin aikin gona da suyi hattara, saboda Kungiyar Boko Haram na saraffa sinadaran

Manoma
Manoma @internet
Talla

Rahotanni a kasar na cewa mayakan Boko Haram na amfani da takin zamani ta hanyar sarrafa shi a ababan hawan su, Sakamakon dakile musu hanyar samun man fetur da Rundunar sojin Najeriya tayi.

Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-haren sari ka noke a wasu jihohin arewacin kasar sanadiyar barin wuta da Rundunar sojin kasar ke yi akan mayakan da nufin cika wa’adin da shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya gindaya na murkushe Boko Haram nan na karshen shekara.

Mutane sama da 4000 ne suka rasa rayukansu tun bayan bullar kungiyar a Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.