Isa ga babban shafi
Najeriya

An kashe ‘Yan Boko Haram 15 a harin sama

Rundunar Sojin saman Najeriya ta sanar da kai harin bam kan tawagar kungiyar Boko Haram a arewacin jihar Barno wanda ya kashe 15 daga cikinsu tare da jikkata wasu da dama.

Najeriya ta kaddamar da harin sama akan Boko Haram
Najeriya ta kaddamar da harin sama akan Boko Haram twitter
Talla

Kakakin sojin saman Ayodele Famuyiwa ya ce jiragen yakin sama a karkashin ‘Operation Gama Aiki’ da aka kaddamar a makon jiya ne suka kai harin kan mayakan kungiyar da ke tserewa daga Dajin Sambisa.

Sannan harin ya jikkata wasu da dama, bayan kashe 15 daga cikin su.

Rundunar sojin kasa da ke fada da ‘Yan Boko Haram a yankin ta tabbatar da adadin mutanen 15 da aka kashe.

A ranar Juma’a ne 19 ga watan Yuni aka kaddamar da jiragen yakin domin yakar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.