Isa ga babban shafi
MDD

‘Yan Gudun hijira na karuwa a duniya

Rikici da yake-yake da kuma tsana ya tursasawa mutane sama da Miliyan 65 kauracewa gidajensu daga karshen shekarar 2015, a cewar rahoton hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Rikici a Burundi ya tursasawa dubbai kauracewa gidajensu zuwa makwabtan kasashe
Rikici a Burundi ya tursasawa dubbai kauracewa gidajensu zuwa makwabtan kasashe AFP Photo/Oxfam/Mary Mndeme
Talla

Rahoton ya ce akalla mutane sama da miliyan 65 aka raba su da matsuguninsu a fadin duniya daga karshen shekarar 2015 abinda ya tilasta mu su zama ‘yan gudun hijira.

Wannan kuma ya faru ne sakamakon yakin Syria da rikicin Afghanistan da Falasdinu da Yemen da Najeriya da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Burundi da Sudan ta kudu da Somalia.

Rahotan ya nuna cewar kashi daya na al’ummar duniya sun gudu sun bar matsuguninsu daga karshen 2015.

Wannan shi ne adadi mafi muni, tun yakin duniya na biyu.

Rahoton ya bayyana damuwa kan yadda ake kyamar ‘yan gudun hijirar, musamman yadda kasashe ke rufe kan iyakokinsu maimakon karbar ‘yan gudun hijirar.

Rahoton ya bayyana cewa cikin minti guda mutane kimanin 24 ke kauracewa gidajensu saboda rikici ko kyamatar addininsu ko kabila.

Majalisar Dinkin duniya tace mutum guda cikin mutane 113 a duniya dan gudun hijira ne, wadanda yanzu suka zarce yawan mutanen Faransa ko kuma Birtaniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.