Isa ga babban shafi
Kenya

MDD ta roki Kenya kan rufe sansanin ‘Yan gudun hijira

Magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya roki hukumomin kasar Kenya da su canza shawara dangane da matakin rufe sansanonin ‘yan gudun hijirar Somalia da ke zaune a kasar.

Sansanin 'Yan gudun hijirar Somalia a Dadaab a Kenya
Sansanin 'Yan gudun hijirar Somalia a Dadaab a Kenya Reuters/Jonathan Ernst
Talla

A wata zantawa ta wayar tarho, Ban Ki-moon ya roki shugaba Uhuru Kenyatta da ya janye wannan mataki, wanda aiwatar da shi zai sa a kori ‘yan gudun hijirar kasar Somalia da ke zaune a Kenya su akalla dubu 600 daga kasar.

Kenya dai ta yanke shawarar rufe sansanonin Dadaab da Kakuma na ‘Yan gudun hijira saboda barazanar mayakan al Qaeda da al Shebaab.

Kimanin ‘Yan gudun hijira dubu dari uku da hamsin ke rayuwa a Sansanin Dadaab da ke kan iyakar Kenya da Somalia.

Yanzu haka kuma Kenya tace ba zata sake karbar ‘Yan gudun hijira ba tare da rufe sansanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.