Isa ga babban shafi
Somalia

Al Shebab ta kashe sojojin Somalia

Rundunar sojin Somalia ta ce, mayakan Al Shebab sun kashe ma ta sojioji 15, sannan kuma suka karbe garin Runirgood da ke yankin arewa maso gabashin birnin Mogadishu a ranar Lahadi.

Mayakan Al Shebab sun kashe sojojin somalia a harin da suka kai sansaninsu a kusa da Mogadishu
Mayakan Al Shebab sun kashe sojojin somalia a harin da suka kai sansaninsu a kusa da Mogadishu © KENYA-SECURITY/SOMALIA REUTERS/Feisal Omar/Files
Talla

Wannan na zuwa ne kwana guda da dakarun gwamnati suka karbe ikon garin mai nisan kilomita 180 daga Mogadishu kamar yadda rundunar ta ce.

Sai dai a nata bangaren, kungiyar Al Shebab wadda ke kokarin kifar da gwamnatin Somalia mai samun goyon bayan kasashen yammacin duniya ta ce, ta hallaka mutane 32 a farmakin na jiya.

Mayakan kungiyar sun yi amfani da wata mota makare da bama-bamai wajen kaddamar da harin na kunar bakin wake a sansanin dakarun soji, kuma jim kadan da tarwatsewar motar, aka fara dauki ba dadi tsakanin bangarorin biyu kamar yadda Manjo Abdullahi Omar ya shaida wa manema labarai.

Manjo Omar ya ce, sojojin sun kashe mayakan guda 10 a ranakun Asabar da Lahadi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.