Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya mayarwa Majalissa kasafin kudi ba tare da sanya hannu ba

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya mayarwa Majalisar Kasar bayanan Kasafin kudin bana ba tare da ya rataba hannu a kai ba, inda ya bukaci a yi gyara a wasu shafukan da bai gamsu da su ba.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Mai magana da yawun majalisar wakilan kasar Abdurrazaq Namdas dake zantawa da manema labarai, ya ce Shugaban ya bukaci Majalisar ta duba wasu sashi na bayanan kudin da ke sabanni abubuwa da ya gabatar.

A na dai cigaba da kace nace kan kasafin kudin Najeriya da har yanzu Shugaba Buhari ya gaggara sanya hannu tun bayan karba cikakken bayanan kasafin daga Majalisar dokoki makwanin biyu da suka gabata.

A bangare guda kuma ana gani cewa rikicin dake kunno kai a majalissun kasar da kuma shari’ar da shugaban majalisar dattijan kasar Bukola Saraki ke fuskanta, sune ke haifar da tsaiko sanya hannu kan wannan kasafi.

Kan wannan batu Umaymah Sani Abdulmumin ta tuntubi tsohon kakkakin Majalisar wakilan kasar Honourable Ghali Umar NaAbba wanda ya bayyana mata mahangarsa.

04:13

Ghali Umar Na'abba

Umaymah Sani Abdulmumin

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.