Isa ga babban shafi
Nigeria

Harin bama-bamai sun kashe mutane 18 a Abuja, Nigeria

A Nigeria, Hukumar kai dauki ta gaggawa NEMA,  ta bayyana cewa mutane 15 suka gamu da ajalinsu, wasu 41 kuma na chan cikin wani hali sakamakon tashin bama-bamai uku a Abuja daren jiya. 

Unguwar Nyanya dake Abuja inda aka taba kai harin Bam
Unguwar Nyanya dake Abuja inda aka taba kai harin Bam rfi
Talla

Bayanai na cewa a yankin Nyanya mutane biyu suka mutu nan take, wasu mutane 21 kuma suka sami munanan raunuka, yayin da a yankin Kuje mutane 13 suka mutu nan take wasu 20 kuma suka jikkata.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na yankin Abuja, Wilson Inalegwu ya shaidawa manema labarai cewa wata ‘yan tatsitsiyar yarinya aka yi amfani da ita wajen kai harin kunar bakin wake a Kuje , yayin da bama-bamai biyu da suka tashi a Nyanya namiji da mace suka tasar dasu a tashar mota.

Babban Sakatare  Mai kula da birnin Abuja John Chuckwu ya nemi mazauna Abuja da su tabbatar da cewa suna sa idanu sosai a duk wuraren da suke harkokin su gudun kada a rika samun wannan labari maras dadi.
Babu wata kungiya da tace ita ta kai wannan hari, amma kuma ana ganin babu wata kungiya da za ta iya wannan bayaga kungiyar Boko Haram saboda ba na farko ba ne kai irin wannan hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.