Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram:Sojoji sun ceto mutane sama da 200

A ci gaba da aiwatar da shirinta na lafiya dole,  Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da ceto mata da yara kanana 241 daga hannun kungiyar Boko.

Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Kasar
Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Kasar REUTERS/Tim Cocks
Talla

Mai Magana da yawun rundunar sojin Kasar Kanar Sani Usman Kukasheka, ya ce zaratan sojojin sun yi nasarar kubutar da matan da yan mata da kuma yaran ne a banki dake kusa da iyakar Kamaru.

Daraktan ya ce yanzu haka jami’an lafiya na tantance lafiyar su.

Matsalar Boko Haram ta addadi kasashen yankin tafkin Chadi kuma dubban jama'a ne suka rasa rayukansu sakamakon hare haren da kungiyar ta kaddamar.

Kasashen yankin tafkin Chadi sun kafa rundunar hadin gwiwa domin murkushe mayakan na Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.