Isa ga babban shafi
Najeriya

An ceto mutane 90 daga hannun Boko Haram a kauyukan Gwoza

Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da ‘yantar mutane 9o daga hannu ‘yan kungiyar Boko haram, bayan da suka fatattaki magoya bayan kungiyar a wasu kauyuka da ke cikin karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Wasu da aka ceto daga hannun Boko Haram a Najeriya.
Wasu da aka ceto daga hannun Boko Haram a Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Mai magana da yawun rundunar tsaron Kanar Sani Usman, ya ce 23 daga wadanda aka ‘yantar maza ne, sai mata 33 da kuma kananan yara 34, kuma lamarin ya faru ne a garuruwan Dissa da kuma Bala-zala da ke kusa da Gwoza.

A baya-bayan nan dai jami’an tsaron Najeriya na samun nasarar ‘yantar da mutanen da kungiyar ta yi garkuwa da su a yankin arewa maso gabashin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.