Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta rasa sakewa a yanzu

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta bayyana cewa Mayakan Boko Haram ba ta da sakewa a yanzu har su samu damar kashe mutane ko kuma karbe sansanonin Sojoji.

Dakarun Najeriya dake yaki da mayakan Boko Haram
Dakarun Najeriya dake yaki da mayakan Boko Haram AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE
Talla

Babban hafson rundunar ne, Saddique Abubakar ya fadi haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taro da aka shirya a babban birnin Abuja.

Abubakar ya kara da cewa rundunar Sojin saman ta yi matukar karya lagwan mayakan na Boko Haram a Arewa maso gabashin Kasar.

Shugaban Kasar dai Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen kungiyar wadda ta salwantar da rayukan al-umma da dama a Najeriya da kasashen dake da makwabtaka da ita da suka hada da Nijar da Kamaru da Chadi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.