Sojojin Najeriya sun kame masu tallafawa Boko Haram
Rundunar Sojin Najeriya shiya ta 25 a Maiduguri Jihar Borno ta bayyana kame wasu mutane 30 da ke tallafawa Mayakan Boko Haram da Abinci a yankin Damboa, kamar yadda kakakin rundunar Kanal Usman Kukasheka ya tattabar wa RFI Hausa.
Wallafawa ranar:
Kukasheka ya ce an kama mutanen dauke da abinci da dama a Korode da za su kai wa mayakan Boko Haram a yankin Damboa zuwa Azir Wajikoro cikin Jihar Borno.
Mutanen da aka cafke sun ce su ‘Yan kasuwa ne ammasun tabbatar da cewa suna kai wa ‘Yan Boko Haram abinci, a cewar Kukasheka.
Dakarun Najeriya dai na samun galaba akan Boko Haram, kamar yadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar a lokacin da ya ke ziyara a Ghana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu