Isa ga babban shafi
Najeriya

Al’ummar Gombe na cikin fargabar harin boko Haram

al'ummar Gombe sun tashi cikin rudani da fargaba sakamakon karar harbe-harben Bindiga da suka ji daga sassa daban daban masu makwabtaka da su

Une habitante de Ngouboua et ses enfants quittent le village.
Une habitante de Ngouboua et ses enfants quittent le village. RFI
Talla

Rahotanni daga garin Gombe na cewar an shiga rudani a wayewar gari yau Assabar bayan da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a wani kauye mai suna Dadin kowa da ke daf da garin gombe.

An ce dai mutane sun gidime ana ta guje-guje, lura da cewar kauyen Dadin kowa na makwabtaka da Gombe ne.

Haka ma karar harbe-harben da aka ji daga bangaren Sojin Najeriya da ‘yan sanda, ya kara firgita jama’a, amma ya zuwa yanzu babu labarin ko wasu sun rasa rayukansu a cikin tashin hankalin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.