Hukumar kare hakkin bil'adama a Najeriya ta gargadi Najeriya kan salwantar da Rayuka
Hukumar kare hakkin bil’adama ta tarayyar Najeriya ta fidda Rahoton cewar ya zuwa yanzu mutane 58 ne suka mutu a gangamin siyasa
Wallafawa ranar:
Wannan kuwa inji rahoton hukumar ya faru ne sakamakon tashe-tashen hankullan da ke da alaka da yadda ake gangamin yakin neman zaben shugaban kasa, gabanin a gudanar da zaben da ake kallo a matsayin zakaran gwajin dafi ga makomar Siyasar kasar.
A rahoton da hukumar ta fitar jiya Jumu’a ta bayyana cewar cikin kwanaki 50 na gangamin yakin neman zaben da aka gudamar, an samu tashin hankalin Siyasa akalla 61 a jihohi 22 na fadin kasar a yayin da mutane 58 suka rasa Rayukansu.
A lokacin da yake gabatar da Rahoton shugaban hukumar Chief Chidi Odinkalu, ya bayyana cewar nauyi ne day a rataya ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ‘yan takara da jam’iyyun Siyasa da kuma jami’an tsaro su tabbatar da kare Rayuwar Tallakawan kasar da suka nuna tsananin kwadayin dorewar Dimokradiyya a cikin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu