Isa ga babban shafi
Chadi

Boko Haram ta kai hari Chadi

Rahotanni daga Chadi sun ce Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari a garin Ngouboua da ke kusa da tabkin Chadi, kuma mayakan sun isa garin ne cikin kwale kwale. Wannan shi ne hari na farko da Mayakan Boko Haram na Najeriya suka kai a Chadi.

Dakarun Chadi a birnin Ndjamena
Dakarun Chadi a birnin Ndjamena Thomas SAMSON/Gamma-Rapho via Getty Images
Talla

Magajin garin ya ce 'yan Boko Haram sun shiga garin ne a cikin dare Alhamis.

Rahotanni kuma sun ce Mayakan na Boko Haram sun kashe mutane akalla 10 kafin Sojojin Chadi su kore su.

Wata majiyar tsaro a Chadi tace kimanin ‘yan Boko Haram 30 ne suka abka wa garin a cikin dare, inda suka kona gidajen mutane.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya yi alkawalin kaddamar da hari Chadi cikin wani sakon bidiyo da ya aiko a Intanet bayan dakarun kasar Chadi sun kori mayakan shi a garin Gamboru da Malam Fatori.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.