Isa ga babban shafi
Nijar

Sojojin Nijar sun murkushe wata ‘yar kunar bakin-wake

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce a jiya Laraba wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake sun kai hari a garin Diffa da ke gabashin kasar, amma sojoji sun bindige daya daga cikinsu kafin ta tarwatsa bam din da ke jikinta.

Dakarun Kamaru da Chadi da ke fada da Boko Haram na Najeriya
Dakarun Kamaru da Chadi da ke fada da Boko Haram na Najeriya RFI/OR
Talla

A cewar majiyar sojan kasar ta Jamhuriyar Nijar, wata mata ce da ke dauke da bama-bamai a jikinta ta yi kokarin kutsawa a cikin jami’an tsaron da ke garin na Diffa, amma bayan da ta ki daga hannayenta sama kamar dai yadda jami’an tsaron suka umurce ta, wannan ya sa aka bindige ta har lahira.

Binciken da jami’an tsaro suka gudanar akan gangar jikinta, shi ne ya tabbatar da cewa matar na dauke da bama-bamai da ta boye a cikin hijabinta.

Kafin nan wani jami’in gwamnati da kuma wasu kafafen yada labarai a garin na Diffa sun tabbatar da cewa wata matar ‘yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta a cikin wata kasuwar kayan miya da ke garin, sai dai ba wanda ya rasa ransa sakamakon hakan illa ‘yar kunar bakin waken.

A ranar litinin da ta gabata ne dai al’ummar garin na Diffa da ke dab da iyaka da Tarayyar Najeriya suka soma ganin harin kunar bakin wake daga ‘yan kungiyar Boko Haram, wadanda suka jima suna bazarana a garuruwan Najeriya da ke kan iyakar Nijar a jihohin Yobe na Borno.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.