Isa ga babban shafi
Boko Haram

Nijar za ta tura dakaru don yakar Boko Haram

Majalisar Janhuriyar Nijar ta amince da bukatar gwamnatin kasar na bayar da gudummawar sojoji don yaki da kungiyar Boko Haram da ke barazanar a kan iyakokin kasashen biyu. Kudirin ya samu amincewar ‘Yan Majalisar kasar da gagarumin ranjaye, kuma Majalisar ta amince a tura dakaru 750 zuwa Najeriya domin yakar Boko Haram.

Kofar Shiga Majalisar dokokin Nijar
Kofar Shiga Majalisar dokokin Nijar AFP/Sia Kambou
Talla

A ranar Assabar ne dai kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Benin da kuma Jamhuriyyar Nijar suka amince da matakin kafa rundunar Soji 8,700 domin yakar Boko Haram.

Rikicin Boko Haram dai yanzu haka ya tsallako zuwa Nijar inda mayakan suka kai wasu hare hare a Jihar Diffa da ke kan iyaka da Najeriya.

01:33

Rahoto: Majalisar Nijar ta amince a tura dakaru don yakar Boko Haram

Lydia Ado

Boko Haram ta kwace ikon garuruwa da dama a Jihohin da ke arewa maso gabacin Najeriya. Rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 13,000 tun fara rikicin a 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.