Isa ga babban shafi
Najeriya

An kama Motoci 2 makare da kuri’u a jihar Zamfara

A Najeriya wasu rahotanni na nuna cewar da yammacin jiya ne aka kama wasu Motoci makare da Takardun kuri’a a birnin Gusan na jihar Zamafara.

INEC
Talla

An dai kama wadannan Motocin ne a cikin garin Gusau kuma ya zuwa lokacin hada wannan Rahoton bamu kai ga samun bayannai a hukumance ba, dangane da wannan batu.

A lokacin da na tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamafara, ya bayyana min cewa a halin yanzu ba shi ya kamata yayi magana ba, amma dai akwai jita-jita da suke ji dangane da haka.

Magudin zabe a tarayyar Najeriya dai ba sabon abu ba ne, kuma akasari, shi ne dalilin tashi-tashina da kan faru bayan bayyana sakamakon zabe a cikin kasar abinda kan yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Gwamanatin jihar Zamafara dai na bukatar a tsananta bincike don gano masu alhakin wadannan Takardun kuri’u.

A zantawarmu da shi kwamishinan watsa labarai na jihar Ibrahim Birnin Magaji, ya ce ba za su bar maganar ta kwana ba.

Sai dai a nata haujin Jam’iyyar PDP a Zamafara a ta Bakin tsohon mai taimakawa tsohon gwamnan Mahmud Aliyu Shinkafi, da kuma tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar ibrahin Dan Maliki, ta karyata labarin da kum abayyana shi a matsayin yaudara irinta Siyasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.