Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar INEC a Nigeria ta ce a shirye take ta yi amfani da na'urori yayin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria INEC, ta ce a shirye take, don yin amfani da na’urorin komfuta, wajen kada kuri’a yayin zabuka masu zuwa, in har dokokin kasar suka bayar da damar hakan. Mataimakn darakta yada labaru na hukumar ta INEC, Nick Dazang yace in har dokokin zaben kasar sun amince da hakan, hukumar zata bi abin da doka ta tsara.Ya ce hukumar bata adawa da amfani da na’urorin zamani wajen gudanar da zaben, amma sai dai dokokin zaben kasar basu bayar da damar hakan ba a yanzu.Ya ce tsarin nada tasiri, musamman ganin yadda hakan ke taka rawa wajen samar da zaben mai inganci, inda yace kasashe kamar su Indiya suna amfani da shi, kuma yana samar da zaben da kowa ke na’am da shi.Mr Dazang yace Nigeria na da yanayi iri daya da kasar ta Indiya, musamman ta yawan jama’a, don haka a cewa shi tsarin zai taimaka matuka.Dama Kungiyar Injiniyoyin karar wato Nigerian Society of Engineers, ko NSE, ta bukaci gwamnatin taraiyya, ta umarci hukumar ta INEC ta fara amfani da tsarin na kada kuri’a ta hanyar na’urori masu kwakwalwa.Kungiyar tace hakan ne kawai zai taimaka wajen kawo karshen matsalar aringizon kuri’a, yayin zabe a kasar. 

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega Reuters/Afolabi Sotunde
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.