Isa ga babban shafi
Nigeria

Hukumar INEC a Najeriya na bukatar naira biliyon 93 don zaben mai zuwa

Hukumar zaben a Tarayyar Najeriya wato INEC, ta ce tana bukatar kudi Naira Bilyan 93 domin gudanar da zaben shekara ta 2015.Shugaban hukumar Fafesa Attahiru Jega ne ya bayyana hakan, lokacin da yake ganawa da Kwamitin Majalisar Dattawan kasar mai kula ayyukan hukumar ta zabe, to sai dai ya ce INEC ba za ta iya gudanar da zaben a cikin jihohi 3 wato Adamawa, Borno da kuma Yobe ba matukar dai suka ci gaba da kasancewa a karkashin dokar ta baci.Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya jiyo Farfesa Jega na cewa, a jimilce mutane milyan 73 da dubu 500 ne za a yi wa rejista domin jefa kuri’unsu a zaben na shekarar 2015 

Reuters/Afolabi Sotunde
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.