Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu dalilin soke zaben Anambra-INEC

Hukumar Zabe a Najeriya tace babu wani dalilin da zai sa ta soke zaben Gwamnan Jahar Anambra, wanda Jam’iyyun siyasa da mutanen kasar suke korafi akai, saboda yan matsalolin da aka samu wadanda hukumar tace ba su taka kara sun karya ba.

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Tuni dai ‘Yan takarar Jam’iyyun PDP da APC da LP wato Tony Nwoye da Chris Ngige da Ifeanyi Ubah suka sha alwashin yin watsi da duk wani sakamako da hukumar zaben za ta bayyana a zaben da aka gudanar a ranakun Assabar da Lahadi a Jahar Anambra.

“Mun san akwai kura-kurai amma kura-kuran ba su zamanto wadanda zasu sa ace zaben be yi kyau ba” a cewar Amina Zakari Jami’ar hukumar Zabe a Najeriya.

Amina ta shaidawa RFI Hausa cewa akwai Matsaloli da suka fuskanta a wasu kananan hukumomi a zaben na Anambra amma tace an gudanar da zaben a kananan hukumomi 20 cikin 21 ba tare da matsala ba.

Alkalumman sakamakon zaben sun nuna cewa dan takarar Jam’iyyar APGA Mai mulki ne a Jahar ke kan gaba William Obiano, da yawan kuri’u amma ba tare da hukumar zaben ta bayyana sunan shi ba a matsayin wanda ya lashe zaben.

Mista Tony Nwoye na PDP shi ne a matsayi na biyu da yawan kuri’u 94,956 sai Dan takarar Jam’iyyar APC Sanata Chris Ngige a matsayi na uku da yawan kuri’u 92,300.

Akwai dai sabanin da aka samu a zaben na Anambra musamman yawan adadin kuri’un da aka soke sun saba yawan adadin da aka kada tsakanin wanda ya lashe zaben da wanda ke bi masa.

Mutanen Najeriya dai suna ganin Zaben Anambra tamkar zakaran gwajin dafi da zai auna ingancin hukumar INEC da kuma farin jinin sabuwar Jam’iyyar gamayyar ‘Yan adawa ta APC da Jam’iyya mai mulki ta PDP a zaben gama gari na 2015.

Babban kalubalen da ke gaban sabuwar Jam’iyyar ‘Yan adawa ta APC, shi ne kawo karshen gwamnatin Jam’iyyar PDP da ke mulki tun da aka dawo mulkin farar hula a 1999.

Tuni hukumar zabe ta INEC ta bukaci Jam’iyyun adawa su kai kokensu kotu game da korafe korafensu akan matsalolin da suka ce an samu a zaben na Anambra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.