Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben Anambra: Zakaran gwajin dafi

Al’ummar Jahar Anambra a kudancin Najeriya sun fara jefa kuri’ar zaben sabon Gwamna, zaben da ake gani tamkar zakaran gwajin dafi da zai auna farin jinin sabuwar Jam’iyyar gamayyar ‘Yan adawa ta APC da kuma Jam’iyya mai mulki ta PDP a zaben gama gari na 2015.

Gwamnan Jahar Anambra, Peter Obi
Gwamnan Jahar Anambra, Peter Obi AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

Babban kalubalen da ke gaban sabuwar Jam’iyyar ‘Yan adawa ta APC, shi ne kawo karshen gwamnatin Jam’iyyar PDP da ke mulki tun da aka dawo mulkin farar hula a 1999.

Jonathan wanda ya fito daga yankin Niger Delta a kudancin Najeriya ana kwarmaton cewa zai sake yin tazarce duk da adawa da shugaban ke fuskanta daga wasu gwamnonin jahohin arewaci na PDP.

Masu fashin bakin siyasa a Najeriya suna ganin zaben Anambra kamar wani zakaran gwajin dafi ne da zai auna ingancin hukumar zabe wajen gudanar da zaben gama gari a 2015.

‘Yan takara 23 ke neman kujerar gwamna a Anambra tun bayan da wa’adin Peter Obi ya kawo karshe bayan ya kwashe shekaru 8 yana shugabanci a Jahar.

Jam’iyyar APGA ita ke mulki a Jahar kuma Obi yana fatar Jam’iyyarsa ta ci gaba da mulki duk da adawa daga Jam’iyyun APC da PDP.

Kakakin hukumar zabe Kayode Idowu yace sun kammala shirin gudanar da zaben tare da samar da dukkanin kayayyakin da ake bukata.

Najeriya dai na cikin kasashen da ke sahun gaba da suka yi kaurin suna wajen yin magudin zabe.

Rahotanni a ranar Juma’a sun ce ‘Yan sandan Jahar Anambra sun cafke mutane sama da 200 da suka shigo daga Jahar Imo da ake zargi an turo su ne domin taimakawa a yi magudi.

Tun da Misalin karfe 8:00 na safe ne aka bude runfunan zabe inda aka fara yi wa masu kada kuri’a rijista. Nasirudden na RFI Hausa yace da misalin karfe 12:00 ne aka fara kada kuri’a.

Sai dai kuma Jami’an tsaron Farin kaya a Najeriya sun cafke Tsohon ministan Abuja Nasiru El Rufa’I jigo a Jam’iyyar Adawa ta APC a garin Awka inda mutanen Jahar Anambra ke jefa kuri’ar zaben Gwamna. Nasirudden yace ana tsare da El Rufa’I a wani masaukin baki mai suna Finotel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.