Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya ce za a binciki harin Baga, Tinubu ya zargi gwamnati

Gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan a Najeriya ta bayar da umarnin gudanar da kwakkwaran bincike akan harin da aka kai a Baga Jahar Borno wanda ya lakume rayukan fararen hula bayan an kwashe sa’oi sama da 24 ba tare da jin ta bakin Gwamnati ba.

Gwamnan Jahar borno Kashim shetimma a lokacin da ya ke kai ziyara a Baga inda aka kai harin da ya kashe mutane 185 a Jahar Borno Arewacin Najeriya
Gwamnan Jahar borno Kashim shetimma a lokacin da ya ke kai ziyara a Baga inda aka kai harin da ya kashe mutane 185 a Jahar Borno Arewacin Najeriya REUTERS
Talla

Mai taimakawa shugaba Jonathan kan harakokin yada labarai Reuben Abbati, yace shugaban ya bayar da umurnin gudanar da cikaken bincike game da kisan.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ma’aikatan tsaron kasar ke cewa Boko Haram ne ta kaddamar da hari kan jami’an tsaro.

Birgediya Janar Olukolade yace bayanan da suka samu shi ne kungiyar Boko Haram ce ta kaddamar da hari, abinda ya sa jami’ansu suka kai wa jama’a dauki.

“Bayanan da mu ke da shi shi ne mutane 25 aka kashe, yayin da muka rasa sojanmu guda wanda ya je ceto rayuwar farar hula” inji Olukolade.

Tsohon Gwamnan Jahar Lagos, Bola Ahmed Tinubu kuma jigo a tawagar ‘Yan adawa, ya zargi Gwamnatin Jonathan da bukatar ganin an ci gaba da samun rikicin Boko Haram saboda biyan wata bukatar Jam’iyyar PDP mai mulki.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin Lagos, Bola Tinubu yace ba ya jin Gwamnatin Jonathan da gaske ta ke wajen ganin an magance matsalar Boko Haram.

“ Akwai gazawa a Gwamnatin tuntuni, domin da ace akwai Gwamnati ta gaskiya kamar yadda ake samu a kasashen da suka ci gaba, shugaba Jonathan da tuntuni ya gudu, domin ya kasa gano tushen kungiyar Boko Haram” a cewar Bola Tinibu.

Harin da aka kai a Baga ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 180.

Wasu bayanai sun ce rundunar Soji da kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi suka kafa don samar da tsaro kan iyakokinsu su ne suka kai harin, ba JTF da ke Maiduguri ba.

Wani daga cikin mutanen da suka tsira da ransu ya karyata rahoton an kashe sojoji 10 a harin na Baga kamar yadda ya shaidawa RFI.

Harin Baga na zuwa ne a dai dai lokacin da ake nazarin sasantawa da Boko Haram don kawo karshen zubar da jini a Arewacin Najeriya.

Dakta Hussaini Abdu na kungiyar Action Aid yace akwai bukatar gwamnati da dauki matakai akan Sojojinta tare da hukunta duk wadanda aka kama da laifi.

"Akwai bukatar gwamnati da dauki matakai akan Sojojinta tare da hukunta duk wadanda aka kama da laifi".

00:41

Dakta Hussaini Abdu na Action Aid

Bashir Ibrahim Idris

Yanzu dai adadin wadanda suka mutu sun haura 3,000 tun fara rikicin Boko Haram a 2009 bayan kisan shugaban kungiyar Muhammed Yusuf da mambobinsu a zamanin mulkin Marigayi Yar’adua.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.