Isa ga babban shafi
Nigeria

Amurka ta gargadi hukumomin Nigeria kan take hakkin dan Adam

Kasar Amurka tayi kira ga gwamnatin shugaban Nigeria Goodluck Jonathan, ta yi hattara don kar ta fada sahun masu keta hakkin bil’adama a Duniya.Amurka dai na nanata kiran ne bayan wanda tayi a baya, sakamakon rahotannin da ke cewar Sojin kasar, na gallazawa tareda kisan wadanda basu ji ba, basu gani ba a fadan da suke da ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram a arewacin kasar.A ranar 14 ga Watan Mayu ne hukumomin kasar suka sanya Dokar TA BACI a jihohi 3 na Arewa maso gabashin kasar, da ake ganin suna zaman mafakar ‘yan kungiyar da ke dauke da makamai.Gwamnatin Najeriyar dai ta kare kanta daga zargin da ake mata, inda ta bayyana matakan da take dauka a matsayin abinda yafi dacewa, a sakamakon halin tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa a kasar. 

Wasu Sojan Nijeriya a garin Baga
Wasu Sojan Nijeriya a garin Baga REUTERS/Tim Cocks
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.