Isa ga babban shafi
Nigeria

Amnesty ta jaddada Matsayinta a kan Kashe jama'a da jami'an tsaron Najeriya ke yi

Kungiyar Amnesty International tayi watsi da sukar da jami’an gwamnatin Nigeria suka mata, kan rahotan da ta fitar wanda yake zargin jami’an tsaro da kashe mutanen da basu ji ba su gani ba, da sunan yaki da Boko Haram.Kungiyar tace ta kwashe shekaru biyu tana tattara bayanai na sunayen mutanen da aka kashe, da wadanda aka kama, da kuma hira da Yan uwan su, kana da ma sunayen jami’an tsaron da ake zargi da aika aikan, kuma ta baiwa hukumomin tsaron Nigeria da kuma gwamnatin kasar dan gudanar da bincike akai.Kungiyar tace, babu yadda za’a asamu zaman lafiya muddin masu hakkin kare doka na karya ta, yayin da kuma kin hukunta wadanda suka aikata ba dai dai ba, kan haifar da daukar fansa. 

wasu gawawwakin mutanen da jami'an tsaro  ke kashewa a Maiduguri
wasu gawawwakin mutanen da jami'an tsaro ke kashewa a Maiduguri Leadership Newspaper
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.