Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Najeriya zata kara da Namibia, Zambia zata kece raini da Sudan

A karshen mako ne kasashen Afrika zasu buga wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya kuma Kasar Zambia da ta lashe kofin Afrika zata kara ne da kasar Sudan a gobe Assabar. kasashen Biyu sun taba haduwa a zagayen Quarter final a gasar cin kofin Afrika, amma kasar Zambia ce ta lallasa Sudan ci 3-0 a birnin Libreville na kasar Gabon a watan Fabrairu.

'Yan wasan kasar Zambia da suka lashe kofin Africa
'Yan wasan kasar Zambia da suka lashe kofin Africa © Reuters
Talla

A yau Juma’a ne kuma kasar Ghana zata kara da Lesotho a birnin Kumasi.
A gobe Assabar ne Najeriya zata kara da Namibia a birnin Calabar, kuma Stephen keshi zai yi amfani ne da matasa masu buga kwallo a gida, domin ya ajiye ‘yan wasa irinsu Taiye Taiwo da John Mikel Obi da Peter Odemwingie.

Matasan ‘yan wasan ne dai Keshi ya yi amfani dasu a wasannin sada zumunci da Najeriya tasha kashi tsakaninta da Masar da kuma Peru. A bara dai Najeriya bata samu shiga gasar cin kofin Afrika ba.

Afrika ta kudu kuma zata kara ne da kasar Habasha.

A birnin Nairobi ne kuma Kenya da Malawi zasu fafata.

Sai dai a kasar Masar saboda zanga-zanga da ke kadawa, ‘Yan wasan kasar zasu buga wasansu ne da Mozambique a birnin Alexandria ba tare da ‘Yan kallo ba.

A ranar Assabar ne a birnin Abidjan, kasar cote d’Ivoire zata karbi bakuncin Tanzania.

A ranar Lahadi ne kuma a birnin Niamey, Jamhuriyyar Nijar zata karbi bakuncin Gabon.

A birnin Yaounde kuma, Kamaru zata kara da Jamhuriyyar Demokradiyar Congo a ranar Assabar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.