Isa ga babban shafi

Gurbatattun allurai da aka yi fasa-kwaurinsu sun kashe yara 10 a Yemen

Akalla yara goma masu fama da cutar sankarar bargo sun mutu a wani asibiti na birnin  Sanaa, babban birnin kasar Yemen. Sun mutu ne bayan da aka yi musu allura mai dauke da  gurbatattun kwayoyi  da aka yi fasa-kwaurinsu, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar a jiya ranar Juma'a.

Wasu daga cikin alluran da aka shigo da su kasar ta Yemen
Wasu daga cikin alluran da aka shigo da su kasar ta Yemen Scott Olson/Getty Images/AFP
Talla

Kasar Yemen dai na fama da daya daga cikin mafi munin rikicin jin kai a duniya, kasar Yemen na fama da karancin magunguna da kayan aikin jinya, sakamakon yakin da ya addabi wannan kasa mai matukar talauci a yankin Larabawa sama da shekaru bakwai.

Wani yaro da ya jikkata a wani hari da jiragen yakin rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta suka kai, yana kwance a wani asibiti da ke Saada na kasar Yemen.
Wani yaro da ya jikkata a wani hari da jiragen yakin rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta suka kai, yana kwance a wani asibiti da ke Saada na kasar Yemen. AP - Hani Mohammed

Rikicin dai ya samo asali ne daga dakarun da ke biyayya ga gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan kawancen da ke karkashin makwabciyarta Saudiyya mai karfi, da 'yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran wadanda suka kwace iko da birnin Sanaa a shekara ta 2014.

Daya daga cikin iyayen yara a kasar Yemen
Daya daga cikin iyayen yara a kasar Yemen AFP - AHMAD AL-BASHA

A wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta 'yan tawayen kasar ta fitar ta ce, "Yara goma da ke dauke da cutar sankarar bargo sun mutu" a asibitin Kuwait, inda ta ce suna cikin rukunin marasa lafiya 19 masu shekaru tsakanin uku zuwa 15 da ke fama da cutar, wadanda kuma yanayinsu ya tabarbare saboda "rashin lafiyar cutar sankarau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.