Isa ga babban shafi

MDD ta koka da gaza sabunta yarjejeniyar zaman lafiya a Yemen

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya roki bangarorin da ke rikici da juna a Yemen su kaucewa duk wani sabani da zai dawo da yakar juna a tsakaninsu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS - UMIT BEKTAS
Talla

Guterres wanda ke wannan kiran bayan rashin nasarar yunkurin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu a ilahirin sassan kasar, ya bukaci bangarorin biyu su shiga tattaunawar da za ta kai ga dawo da yarjejeniyar.

Kakakin majalisar dinkin duniyar Stephane Dujarric ta ruwaito Guterres na bayyana takaicinsa da yadda gwamnatin kasar mai samun goyon bayan kasashen Duniya ta gaza sabunta yarjejeniyar da ke tsakaninta da ‘yan tawayen Houthi har zuwa 2 ga watan da muke ciki na Oktoba lokacin da yarjejeniyar ta kawo karshe.

A cewar Guterres yarjejeniyar tsagaita wutar watanni 2 da bangarorin biyu suka kulla a ranar 2 ga watan Aprilu aka kuma tsawaita ta har sau biyu ta taimaka matuka wajen rage zubar da jinni a rikicin bangarorin biyu.

Sai dai Majalisar ta bayyana takaici kan yadda rashin sake tsawaita yarjejeniyar a yanzu ka iya haifar da dawowar rikicin bangarorin biyu, mafi muni da wata kasa a gabas ta tsakiya ta fuskanta.

Yemen da ke sahun kasashe mafiya talauci a Duniya, tun shekarar 2014 ta ke fama da yakin basasa tsakanin dakarun gwamnatin kasar masu samun goyon bayan kasashen larabawa da kuma ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.