Isa ga babban shafi

An gaza kammala zaben Brazil a zagayen farko

Za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugancin kasar Brazil a ranar 30 ga watan Oktoba, bayan da jagoran ‘yan adawa Inacio Lula da Silva ya doke shugaba mai ci Jair Bolsonaro a zagayen farko, amma da tazarar da ba ta isa bashi nasarar lashe zaben kai tsaye ba.

Tsohon shugaban Brazil Inacio Lula da Silve da ke neman a sake zabensa (Hagu), tare da shugaba mai ci Jair Bolsonaro
Tsohon shugaban Brazil Inacio Lula da Silve da ke neman a sake zabensa (Hagu), tare da shugaba mai ci Jair Bolsonaro AFP - EVARISTO SA
Talla

Sakamakon zagayen farko na zaben kasar ta Brazil ya nuna cewar, Lula da Silva da ke neman a sake zabensa karo na biyu a matsayin shugaban kasa, ya samu kashi 48.4 na kuri’un da aka kada, yayin da shugaba Bolsonaro ya samu kashi 43.2, bayan da aka kidaya kashi 99 cikin 100 na kuri’un da aka kada a rumfunan zaben kasar.

Lula, ya jagoranci kasar Brazil ne daga shekarar 2003 zuwa 2010.

Gabanin zaben na ranar Lahadi, wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta yi hasashen cewa tsohon shugaba Lula zai samu kashi 50 na kuri’un da za a kada, yayin da Bolsonaro zai samu kashi 36.

Sakamakon dai ya kasance na ba zata ga shugaba Bolsonaro mai ra’ayin rikau, la’akari da kwarin gwiwar da ya dade yana nanatawa kan samun  nasara a zaben da yake fatan ganin ya zarce bisa shugabancin Brazil.

Dole ne dai sai dan takara ya samu fiye da kashi 50 na kuri’u kafin samun nasarar kai tsaye a zaben na Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.