Isa ga babban shafi

Al'ummar Brazil na cigaba da nuna matsayarsu kan wanda zai rike shugabancin kasar

'Yan Kasar Brazil yau na kada kuri’ar zaben shugaban kasa, a zaben da ake fafatawa tsakanin shugaba Jair Bolsonaro da tsohon shugaban kasa Inacio Lula da Silva.

Lula da Bolsonaro kenan da ke neman shugabancin kasar Brazil
Lula da Bolsonaro kenan da ke neman shugabancin kasar Brazil © Fotomontagem com fotos da AP/ Andre Penner/Andre Coelho
Talla

Lula mai shekaru 76, da ya shugabanci kasar a shekara ta 2000 ya kuma bunkasa tattalin arzikin ta ya bayyana aniyarsa na dawo da kimar Brazil saboda abinda ya kira fita hayyacin ta da tayi a karkashin jagorancin tsohon Kaftinm na soji Bolsonaro mai shekaru 67.

Bolsonaro ya kada kuri’ar sa a Rio de Janeiro sanye da rigar kwallon kasar, inda yace za’a amince da sakamakon zaben muddin aka tabbatar da sahihancinsa.

Shugaban Hukumar zabe Alexandre de Moraes ya yaba da yadda zaben ke gudana, musamman abinda ya shafi ingancin sa da tsaro da kuma yadda ake amfani da na’urorin kada kuri’a.

Akalla jami’an tsaro sama da dubu 500 aka girke domin tabbatar da zaman lafiya lokacin kada kuri’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.