Isa ga babban shafi

An tashi baram-baram a muhawara tsakanin Bolsonaro da Lula gabanin zaben Brazil

Gidan jaridar da ya tsara muhawara tsakanin ‘yan takarar shugabancin kasar Brazil ya bayyana takaici kan yadda Bolsonaro da Lula de Silva, suka keta dokokin da muhawarar ta tanada bayan jifan juna da zafafan kalamai marasa dadi a zauren muhawarar ta jiya alhamis, inda dukkaninsu suka zargi juna da sharara karairayi da kuma son rai baya ga cin hanci da rashawa.

Bolsonaro da Lula de Silva na matsayin manyan 'yan takarar da za su fafata a zaben na gobe lahadi.
Bolsonaro da Lula de Silva na matsayin manyan 'yan takarar da za su fafata a zaben na gobe lahadi. AP
Talla

Shugaba Jair Bolsonaro na jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi da ke neman wa’adi na biyu a mulkin Brazil zai kara ne da Luiz Inacio Lula de Silva a zaben na jibi lahadi bangarorin da ke matsayin manyan ‘yan adawa a kasar tsawon shekaru.

Yayin muhawarar ta ranar alhamis wadda ta juye zuwa fadar zafafan maganganu ga juna, shugaba Jair Bolsonaro da ke fuskantar zarge-zargen Rashawa musamman daga bangarorin ‘yan adawa, ya zargi tsohon shugaban kasar Lula da kasancewa maci amanar kasa baya ga zamowa makaryaci kuma tsohon dan gidan yari.

A bangare guda Lula na jam’iyyar masu sassaucin ra’ayi, da ya mulki Brazil daga shekarar 2003 zuwa 2010 da ke ikirarin samun gagarumar nasara kan Bolsonaro a tashin farko ya bayyana shugaban mai ci a matsayin dan. rashawa da ke nuna son rai a salon mukinsa.

A cewar Lula da Silva, abin kunya ne a koda yaushe karya ta rika fitowa daga bakin mutumin da ya ke kiran kansa shugaba, dalilin da a cewarsa na daga cikin abubuwan da za su kawar da tsohon makerin daga kujerarsa ta mulkin Brazil.

Dan jaridar da ke jagorantar zaman muhawarar William Bonner ya ce bangarorin biyu sun karya ka’idojin da muhawarar ta kunsa ta hanyar mayar da ita rikici sabanin gamsar da masu kada kuri’a da aka tsara domin yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.